'Tottenham ba ta nemi kocin Ajax ba'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin Tottenham mai-ci Tim Sherwood yana da kwantaragi da kulob din har zuwa badi.

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta ce sam ba gaskiya ba ne cewa ta tuntubi kungiyar Ajax da maganar neman kocinta Frank De Boer.

A ranar Talata ne mai magana da yawun kungiyar ta Ajax ya ce Tottenham din ta tuntube su tana bincikar yiwuwar samun Boer din.

Sai dai a cikin wata hira da BBC mai magana da yawun kulob din na Tottenham ya ce ''ba mu tuntubi kowane kulob ba da sunan neman koci. Mun yi nadamar da ya zama dole ne mu yi wannan bayanin''

A ranar Lahadi De Boer ya jagoranci Ajax ta lashe gasar zakarun kungiyoyin kasar Holland a karo na hudu a jere tun bayan da ya karbi jagorancin kungiyar ta birnin Amsterdam.

Karin bayani