Babu matsala kan raunin Rooney

Hakkin mallakar hoto f
Image caption Wayne Rooney

Wayne Rooney zai iya shiga cikin tawagar 'yan kwallon Ingila, duk da cewar yana fama da rauni a halin yanzu.

A cikin wannan watan ne kocin Ingila, Roy Hodgson zai fitar da jerin 'yan wasan da za su wakilci kasar a gasar cin kofin duniya.

Rooney dan wasan Manchester United ya ji rauni, kuma kocinsa na riko Ryan Giggs ya ce ba zai buga karawarsu da Sunderland ba a ranar Asabar.

Ingila na fuskantar matsalar 'yan wasan da ke fama da rauni a yayinda ake shirye-shiryen gasar cin kofin duniya a Brazil.

Wasu daga 'yan wasan da ke fama da rauni sun hada da Townsend da Walcott da kuma Rodriguez.

Karin bayani