Mourinho ya soki Eden Hazard

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Eden Hazard

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya ce akwai ayar tambaya a kan maida hankalin Eden Hazard wajen wasanni.

Mourinho ya ce kamata ya yi Hazard ya rike Juanfran wanda ya farkewa Atletico Madrid kwallo, a wasan da aka doke Chelsea da ci uku da daya.

Hazard mai shekaru 23, ya soki salon taka ledar Chelsea.

Mourinho ya maida martani da cewar "Eden ya nuna cewar ba zai iya sadaukar da kai a kan tawagar ba".

Chelsea na shirin fuskantar Norwich a wasan Premier a ranar Lahadi.

Karin bayani