Man City ta kama hanyar daukar Premier

Image caption Nasarar ita ce ta biyu a haduwar Man City da Everton 15 a Goodison

Manchester City ta kama hanyar lashe gasar Premier da ta sake dawowa matsayin ta daya bayan ta doke Everton 3-2.

Kungiyar ta kawar da Liverpool daga matsayin ne da bambancin yawan kwallaye 59 da 50,amma maki 80 kowacce ke da shi a wasanni 36.

Ross Barkley ne ya fara ci wa Everton kwallo a wasanta na 37, a minti na 11, kafin Aguero ya rama a minti na 22.

Dzeko ya ci wa Man City ta biyu mintina biyu kafin hutun rabin lokaci kuma ya kara a minti uku da dawowa.

Ita kuwa Everton, Lukaku ne ya ci mata kwallonta ta biyu a minti na 65.

Karin bayani