An fitar da Fulham daga rukunin Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Koc Magath na jin 'yan wasansa ne ba su buga wasan yadda za su yi nasara ba.

An fitar da kulob din Fulham daga rukunin gasar Premier bayan kwashe shekaru 13 yana fafatawa a matakin.

Kungiyar da ke yammacin London ta fado ne daga rukunin sakamakon kashin ci 4-1 da ta sha hannunStoke City da kuma nasarar da Sunderland ta samu kan Manchester United.

Kocin kungiyar Felix Magath ya ce ita ce wasa mafi muni da yaransa suka buga tun zuwansa kulob din.

A ranar Lahadi mai zuwa ne Fulham za ta buga wasanta na karshe a matakin na Premier da Crystal Palace kafin ta koma rukunin Championship a karon farko cikin shekaru 13.

Karin bayani