Man' City: 'Har yanzu da saura'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Man' city dai ta sha gaban Liverpool ne kan teburin gasar da bambancn kwallaye.

Manajan Kulob din Manchestar City Manuel Pellegrini ya gargadi 'yan wasansa cewa ka da su dauka sun lashe kambun gasar Premier duk da doke Everton da suka yi.

Yanzu dai City din ce ke kan gaba a gasar bisa bambamcin yawan kwallaye kuma suna iya lashe kambun idan suka ci dukanin wasanni biyun suka rage musu.

Za su buga wasanni biyu da Aston Villa kuma West Ham duka a filinsu na Etihad Stadium a makon karshen na gasar.

'' Wannan (nasarar) babban ci-gaba ne a wajen lashe kambun amma sakona shi ne har yanzu wasa bai kare ba.'' Inji Pellegrini.

Karin bayani