An sassauta hukuncin da aka yankewa Blake

Image caption An zabi Blake domin ta fafata a gasar Olympics ta London amma wannan haramcin ya hana ta shiga ba.

An sassauta haramcin shiga wasanni na shekaru 6 da aka saka wa 'yar tseren mita 400 ta kasar Jamaica Dominique Blake zuwa shekaru 4 da rabi.

Kotun hukunta laifukkan da suka shafi wasanni ta ce ta sassauta hukuncin ne saboda haramcin shekaru 6 da Hukumar Yaki da Shan kwayoyin kara kuzari ta kasar Jamaica ta saka mata yayi tsauri sosai.

An samu Blake ta sha sanadarin methylhexaneamine, wani maganin kara kuzari da aka haramta a watan Yuni shekara ta 2012 yayin jarraba 'yan wasan da za su je gasar Olympics.

Dominique Blake dai ta daukaka kara ne zuwa kotun bayan hukuncin da hukumar ta kasar Jamaica ta yanke, sai dai duk da haka ba ta za koma shiga wata gasa ba sai farkon 2017.

Karin bayani