'Chelsea na bukatar dan wasa mai kisa'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Chelsea na matsayin ta uku ne a teburin gasar Premier.

Manajan Kulob din Chelsea Jose Mourinho ya ce kulob din na bukatar dan wasan gaba mai kisa domin kashe abokan gaba masu taurin kai a zango wasanni mai zuwa.

Fatan Chelsea na daukar kambun gasar Premier ya dushe bayan canjaras din da suka yi na Norwich.

A kwanan bayan ma ta sha kashi hannun Aston Villa da Crystal Palace da kuma Sunderland.

''Ba mu da irin dan wasan nan da idan ya samu 'yar kafa ko yaya take, zai iya cin kwallo, ya bude kofa'' Inji Mourinho

Karin bayani