Murray zai dauki McEnroe a zaman koci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yanzu Murray na shirin karawa da Nicolas Almagro a gasar Barcelona Open a Madrid.

Andy Murray na tunanin dauko John MacEnroe a zaman kocinsa bayan da ya nuna sha'awar aiki da shi.

Zakaran na wasan Tennis ta Winbledon, Murray, ya kasance ba tare da mai bashi horo ba tun bayan da suka rabu da Ivan Lendl a watan Maris.

McEnroe dan kasar Amurka mai shekaru 55, ya lashe gasar Grand Slam har sau bakwai lokacin da yake dan wasa.

Murray zai dauki kocin kafin soma gasar French Open da za a fara ranar 25 ga watan Mayu, amma zai jira har karshen gasar Wimbledon, wadda ta za a kammala ranar 6 ga watan Yuli kafin su fara aiki tare.

Karin bayani