Liverpool: 'An gama da mu a Premier'

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Luis Suarez dai ya bar filin wasan ne cikin hawaye sakamakon canjaras din da suka yi.

Manajan kungiyar Kwallon kafa ta Liverpool Bredan Rogers, ya ce damar da kulob din ya samu ta daukar kambun gasar Premier ta bana ta riga ta gushe; bayan canjaras 3-3 da suka yi da Crystal Palace.

Ya ce babu abin da suke bukata illa su ci wasan amma ba samu hakan ba; ya kara da cewa '' Ko shakka babu Manchester City ce za ta dauki kambun''

Sai dai Liverpool din ta jagoranci wasan ta daren Litinin da ci 3-0, amma sai Crystal Palace ta waiwayo ta rama duka kwallayen uku da aka jefa mata.

Liverpool ce dai ke saman teburin gasar da tazarar maki daya kacal a gaban Manchester City, wadda ke da wasanni biyu da za ta buga a gaba kuma tana da fifikon yawan kwallaye.

Karin bayani