Mace ta zamo koci a kulob din maza

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption macen da ta zama koci a kasar faransa ta kuma kware wajen zabo yan wasa

Kulob din Clermont Foot na Kasar Faransa ya nada wata mace mai suna Helena Costa a matsayin kocinsa, abin da ya sa ta zamo mace mafi girman matsayi a kungiyoyin kwallon kafa na Turai.

Costa, wadda tsohuwar mai jarraba kwarewar 'yan wasa ce ga kulob din Celtic, ta kuma kasance mai horas da kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Iran tun shekarar 2012.

Helena 'yar kasar Portugal mai shekaru 36, za ta kama aiki gadan-gadan da Kulob din na Clermont a karshen wannan kaka.

Kulub din mai buga wasa a rukunin Ligue 2 ta Faransar ya ce hakan zai taimaka masa shiga wani sabon zamani.

Karin bayani