Giggs ya ce martabar Man' U za ta dawo

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Har yanzu dai United na da wata dama ta samun tikitin shiga gasar zakarun Turai da za a yi nan gaba.

Kocin rikon-kwarya na Manchester United Ryan Giggs ya fadawa magoya bayansu cewa su sha kurumin su, nasara na tafe nan gaba bayan da kungiyar ta kare a matsayin ta bakwai a gasar Premier.

A wani jawabi da ya gabatar mai sanyaya zuciya a filin wasa na Old Trafford bayan kammala wasan su na karshe a gida, Giggs yace ''Gasar bana ta kasance mai wahala a gare mu, amma muna sa ran nasara ba da dadewa ba. Nasarorin da muka samu a shekarun baya su ne suka sangarta mu.''

Giggs, mai shekaru 40, ya gabatar da jawabin ne bayan nasarar da kulob din ya samu kan Hull City ta ci 3-1 wanda kuma ake sa ran ita ce bayyanar sa ta karshe a filin.

Giggs, wanda har yanzu bai fayyace ko zai ci gaba da zama a United din ba ko a'a, ya shigo wasan nebayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

'

Karin bayani