Pellegrini yana sa ran cin gasar premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Man City ta jefa kwallaye 100 a gasar Premier

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini na sa ran kulob din sa zai lashe gasar Premier a wasan da suka yi ranar Lahadi inda ya ce sun taka rawar gani.

Nasarar da kulob din ya samu na lallasa Aston Villa da ci 4-0, na nufin kulob din ya dara West Ham da maki daya a wasan karshe , kuma City na iya lashe gasar a karo na biyu a kakar wasanni uku.

Pellegrini ya ce "kamar yadda cin kofin ke da muhimmanci, kuma ma irin kokarin da za mu yi mu na lashe gasar."

City ta kasance a saman tebur kwanaki 11 kafin nasarar da suka samu kan Villa wanda da ita ce suka cike adadin kwallaye 100 da suka jefa a raga a gasar Premier.