Wenger ya jinjinawa Man City

Arsene Wenger
Image caption Manchester ta zura kwallaye 100 a raga

Manajan Arsenal Arsene Wenger ya ce abin al'ajabi ne ace Manchester City bata lashe gasar Premier League ba sannan ya taya kulab din murnar nasarar da suka samu.

Da matukar al'ajabi idan suka kasa lashe gasar a yanzu in ji Wenger

Manchester City wacce ta zura kwallaye 100 a wannan kakar wasannin, na bukatar maki daya kachal a gida ga West Ham a ranar Lahadi domin ta kare kambunta.