Brazil: Jones da Rooney za su yi wasa

Wayne Rooney da Phil Jones Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jones ma ba zai buga wasan ba, saboda da zai tafi Southampton.

Kocin rikon kwarya na kungiyar Manchester United, Ryan Giggs ya ce Wayne Rooney da Phil Jones sun murmure, kuma za su iya bugawa Ingila wasa, a gasar cin kofin Duniya da za a yi a Brazil.

Jones mai shekaru 22 kuma dan wasan bayan United, ya samu rauni a kafadarsa a wasan da Manchester United ta doke Hull City da ci 3-1, shi ma Rooney mai shekaru 28 ya ji rauni a matse-matsinsa.

A ranar Litinin mai zuwa ne ake sa ran kocin Ingila Roy Hodgson, zai bayyana sunayen 'yan wasa 30, da za su buga wa kasar wasa a gasar cin kofin duniyan.

Giggs ya ce "Yanzu haka Rooney ya fara yin horo, zai kuma kara warwarewa kafin lokacin gasar."

Ryan Giggs ya kara da cewa, bai dade da fara horon ba, saboda haka zai yi wahala a ce ya warke gaba daya nan da ranar Lahadi.