AC Milan: An jefawa 'yan wasa ayaba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Nigel De Jong ya dauki ayaba da aka jefa a filin wasa .

Magoya bayan 'yan wasan Atalanta sun jefawa 'yan wasan AC Milan ayaba a ranar Lahadi.

Dan wasan kasa da kasa na Guinea Kevin Constanta da kuma dan wasan tsakiyar Netherlands Nigel De Jong sun dauki ayaba guda biyu da aka jefa a filin wasa .

Bayan lamarin, an yiwa magoya bayan Atalanta gargadin cewa za a iya dakatar da wasan wanda Atalanta ta lashe da ci 2 da 1 idan aka sake samun aukuwar hakan.

A makonni biyu da suka gabata dan wasan bayan Barcelona dan kasar Brazil Dani Alves ya dauki wata ayaba da aka jefa masa sannan yaci.