'Dzeko ya cancanci gwarzon dan wasa'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho ya ce Dzeko ne zabin sa

Manajan Chelsea Jose Mourinho ya yi ikirarin cewa dan wasan Manchester City Edin Dzeko ne ya cancanci zama gwarzon dan wasa na wannan shekarar fiye da Luis Suarez na Liverpool.

Suarez dan shekaru 27 ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniyar ta kungiyar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa kuma zai karbi lambar yabo a ranar Alhamis.

Mourinho ya ce idan Manchester ne zakarun Premier, to dan wasan Man City ya kamata a baiwa kyautar gwarzon dan wasa, kuma zabi na shine Dzeko.

City na bukatar maki daya kachal a gida a ranar Lahadi domin kare kanbunsu, amma idan hakan bata samu ba, Liverpool zata iya kwace kanbun idan har ta doke Newcastle a Anfield.