Afirka ta Kudu na son karbar bakuncin gasar kofin duniya

Hakkin mallakar hoto ALL SPORT
Image caption Afirka Ta Kudun ce zata karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 20 a shekarar 2016

Afirka ta Kudu ta bayyana sha'awarta na karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafar duniya ta mata a shekarar 2019.

Hukumar kwallon kafar duniya FIFA ta bayyana cewa ta sami irin wannan bukata daga kasashen Ingila da Faransa da Jamhuriyar Korea da kuma New Zealand.

Kuma ga alamu wadannan kasashe hudu sune zasu kasance a gaba a cikin kasashen dake nuna sha'awarsu, saboda tuni Afirka Ta Kudun ta shirya tsaf domin karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafar duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 20 a shekarar 2016.

FIFA zata so ace gasar cin kofin duniyar na mata 'yan kasa da shekaru 20 a shekara ta 2018 da kuma gasar cin kofin duniyar shekara ta 2019 a karbi bakuncinsu a kasa guda.