Fifa na son a dauki mataki kan jifa da ayaba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan kallo sun jefawa 'yan wasan AC Milan ayaba a ranar Lahadi

Shugaban Fifa Sepp Blatter ya yi kira akan hukumar kwallon kafar Italiya data dauki mataki bayan da magoya bayan Atalanta suka jefawa 'yan wasan AC Milan ayaba.

Shugaban Fifan ya kuma bukaci wani martani daga kungiyar kwallon kafa ta Rasha bayan da wani dan kallo ya naushi wani dan wasan Dinamo Moscow a lokacin wasan su da Zenit St Petersburg.

Blatter ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa dole ne hukumomi su dauki mataki akan banbacin launin fata.

Wannan shine karo na uku a cikin karshen makonni har uku da ake jefa ayaba akan dan wasa yayin wani wasa na Serie A da aka buga a ranar Lahadi.

Har yanzu hukumar kwallon kafa ta Italiya bata fitar da wani martani ba dangane da abinda ya faru a ranar Lahadin.