An sa Aston Villa a kasuwa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Randy Lerner ya sai kulab din daga Doug Ellis

Mutumin dake mallakar kulab din Aston Villa Randy Lerner ya sanar da cewa an sa Kulab din na Premier League a kasuwa.

A wata sanarwa da ya fitar, ya ce 'idan har a raina ina jin cewa ba zan iya cigaba da yin aikin ba, akwai hakkin Villa akaina na ganin cewa kulab din ya cigaba, sannan ya samu shugabanci nagartacce'

Kulab din Aston Villa ya kammala wannan kakar wasannin da matsayi na 15.

A watan da ya gabata be Lerner wanda ya sai kulab din daga Doug Ellis, ya bayyana cewa zai yi bayani game da rade radin da ake tayi game da makomar sa a kulab din a wannan kakar wasannin.