Liverpool na zawarcin Adam Lallana

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Adam Lallana da Luke Shaw

Kungiyar Liverpool ta zawarcin dan kwallon Southampton, Adam Lallana, kamar yadda BBC ta gano.

Lallana mai shekaru 26, na cikin tawagar Southampton a kakar wasa ta bana, kuma ya zura kwallaye 10 a cikin wasanni 42.

Ana saran zai kasance cikin 'yan wasan da Ingila za ta gayyata domin buga gasar cin kofin duniya a Brazil.

Lallana ya ce "Ina son in buga gasar cin kofin zakarun Turai".

Wasu rahotanni kuma sun bayyana cewar Manchester United ta bada tayin fan miliyan 27 don sayen dan kwallon Southampton Luke Shaw.

Bisa dukkan alamu dai, manyan kungiyoyi za su kwashe matasan 'yan kwallon Southampton da suka haskaka a kakar wasa ta bana.