'Ingila zata iya kaiwa zagayen kusa dana karshe'

Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Alan Shearer shine tsohon Kyeptin din Ingila

Tsohon Kyeptin din Ingila Alan Shearer ya ce ya yi murna da tawagar da zata je gasar cin kofin duniya karkashin jagorancin Roy Hodgson, kuma ya yi imanin cewa 'yan wasan zasu iya kaiwa ga wasan kusa dana karshe.

Hodgson dai ya bayyana sunayen 'yan wasa 23 da zasu je Brazil, cikinsu har da dan wasan tsakiyar kulab din Everton Ross Barkley mai shekaru 20.

Shearer ya kuma shaidawa BBC cewa 'akwai abin sha'awa ganin matasa cikin tawagar, wadanda keda 'yar kwarewa'.

Da mutane irin su Wayne Rooney za a iya kaiwa ga wannan matsayi a ganin Shearer