''Yan Man U sun yi wa Moyes komai'

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption An sallami Moyes a watan da ya gabata

Nemanja Vidic ya yi watsi da zargin da ake na cewa 'yan wasan Man United sun daina taimakawa tsohon kocin kulob din Davis Moyes.

A wata doguwar hira da yayi da BBC Vidic ya bayyana irin cece-kucen da ya faru a dakin saka kaya na 'yan wasa tsakanin su a lokacin da gasar ta yi muni.

Amma ya musanta fadin munanan kalamai masu nuna rashin da'a ga kocin.

Ya ce babu alamar tambaya akan kowane dan wasa domin sun yi duk abinda aka neme su da su yi

An sallami Moyes a watan da ya gabata kasa da shekara guda bayan an tabbatar da shi a matsayin magajin Sir Alex Ferguson.