Wenger: Wasan karshe ba shi da tasiri

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wenger ya kammala kwanturagin sa a wannan kakar wasannin

Manajan Arsenal Arsene Wenger ya ce wasan karshe na kofin FA na ranar asabar da suka yi da Hull City ba zai yi tasiri akan makomarsa ba.

Wenger mai shekaru 64 ya kammala kwanturagin sa a wannan kakar wasannin amma ya jinkirta sanya hannu akan sabuwar yarjejeniya duk kuwa da rade radin da aka yi a makon da ya gabata cewa zai zauna a Arsenal .

Da aka tambaye shi ko ya wasan su na karshe zai yi tasiri a makomarsa, Wenger ya bada amsar cewa babu wani tasiri, yana mai jaddada cewa babu wani canji game da kwanturagin sa.

Tun lokacin da suka dauki kofin FA bayan bugun daga kai sai mai tsaron gida akan Manchester United a shekarar 2005, 'yan wasan Arsenal sun sha kashi a shekarar 2006 a wasan karshe na Champions League da suka buga da Barcelona da kuma wasan karshe na kofin League da suka buga da Chelsea a shekarar 2007 da kuma Birmingham City a shekarar 2011.