Suarez ya musanta barin Liverpool

Luis Suarez Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Luis Suarez ya ce yanzu hankalinsa ya karkata ne kan gasar cin kofin duniya

Dan wasan gaban kungiyar Liverpool Luis Suarez, ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa zai bar kulob din a lokacin bazara.

Suarez mai shekaru 27 dan asalin kasar Uruguay, ya rattaba hannu kan sabuwar kwantaragin shekara hudu da rabi a watan Disamba

Ya kuma musanta cewa akwai wata doka data bashi damar hadewa da Real Madrid da kuma Barcelona a wannan kakar wasannin.

Ya ce 'a yanzu na maida hankali ne akan gasar cin kofin duniya'.

Dan wasan ya koma Liverpool bayan ya bar Ajex a shekarar 2011 kan kudi fam miliyan 22.

Tun a bazarar bara ya so barin kulob din, inda Arsenal ta yi masa tayin fam miliyan 40 da doriya, bisa tsammanin akwai wannan kafar a kwantiraginsa.