Ingila:Lampard ne mataimakin kyaftin

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ingila za ta buga wasa da Italiya a Brazil

Frank Lampard ne zai kasance mataimakin Kyaftin din 'yan wasan Ingila a gasar cin kofin duniya a Brazil, kamar yadda kocin Ingila Roy Hodgson ya bayyana.

Dan wasan tsakiyar Chelsea mai shekaru 35 zai kasance mataimaki ga Steven Gerrard.

Lampard ya rike mukamin Kyaftin ga Ingila har sau shida.

Ingila za ta yi wasannin sada zumunci uku da Kasashen Peru da Ecuador da Honduras kafin soma buga gasar cin kofin duniya a ranar 14 ga watan Yuni da Kasar Italiya.