Juventus ta kafa sabon tarihi a Turai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan wasan Juventus na murnar lashe gasar Serie A

Juventus ta kafa wani sabon tarihi a kwallon kafar Turai inda ta samu maki 102 wajen lashe gasar Serie A, watau fiye da duk wata kungiya da ke manyan gasa 10 a nahiyar.

Juvetus ta baiwa Roma wacce ke matakin na biyu tazarar maki 17 a kakar wasan da aka kamalla, inda Juve din ta lashe wasanni 19 cikin 19 da ta buga a gidanta kuma ta samu nasara a wasanni 33 a gasar.

Wannan tarihin, ya sa Juventus ta shiga gaban Barcelona da Real Madrid da Chelsea da kuma Bayern Munich a kokarin lashe gasa.

Kocin Juve, Antino Conte wanda kawo yanzu ya ki sabunta kwangilarsa a kungiyar, ya samu jinjina daga wajen 'yan kallo.

Karin bayani