Messi zai cigaba da zama a Barcelona

Hakkin mallakar hoto d
Image caption An bada rahotan cewa Messi ya bukaci ya zama dan wasan da ya fi kowanne dan wasa a duniya karbar kudade masu tsoka

Gwarzon dan wasan duniya na shekara har sau hudu Lionel Messi ya sanya hannu akan sabon kwanturagi tare da Barcelona.

Messi ya bayyana farincikinsa a lokacin da yake sanya hannun sabon kwanturagi da Barcelona a ranar Litinin

Sai dai har yanzu babu cikakken bayani game da tsayin sabon kwanturagin, tare da dan wasan gaban mai shekaru 26 wanda ya zura kwallaye 44 a raga a kakar wasannin data gabata.

Kwanturagin da ya sanyawa hannu a karshe wacce aka amince da ita a watan fabairun bara, zata kai shekarar 2018.

Barcelona ta sanar a ranar Juma'a cewa an amince da sabon kwanturagin bayan tattaunawa mai tsaho a inda aka bada rahotan cewa Messi ya bukaci ya zama dan wasan da ya fi kowanne dan wasa a duniya karbar kudade masu tsoka