Takaddama a kan mukamin koci Saliyo

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption 'Yan wasan Saliyo sun sha kashi a cikin gida da ci 2-0 a hannun 'yan wasan Ghana

Ana cigaba da samun baraka tsakanin hukumar kwallon kafa ta Saliyo da kuma ma'aikatar wasannin kasar .

A wannan karon barakar ta kunno kai ne dangane da mai horar da 'yan wasa na 'yan kasa da shekaru 20.

Kowacce hukuma ta bayyana kochin 'yan wasan gabanin gasar zakarun nahiyar Afirka na 'yan kasa da shekaru 20 da za a yi ranar asabar zagayen farko a Ghana.

Hukumar kwallon kafar Saliyo ta hakikance cewa Alimamy Turay har yanzu shine kochin 'yan kasa da shekaru 20, duk kuwa da sanarwar da ministan wasannin kasar Paul Kamara ya yi na cewar an kore shi.

Ministan ya bayyana sunan tsohon dan wasan kasa da kasa na Saliyo Atto Mensah a matsayin wanda zai maye gurbin Turay bayan da 'yan wasan kasar suka sha kashi a cikin gida da ci 2-0 a hannun 'yan wasan Ghana.