Craig Gardner zai hade da West Brom

West Brom ta jima tana harin Craig Gardner

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

West Brom ta jima tana harin Craig Gardner

West Brom ta sanya hannu na daukar dan wasan tsakiyar nan Craig Gardner daga kulab din Sunderland a wata yarjejeniya ta shekaru uku.

Tsohon dan wasan Aston Villa dan shekaru 27 zai hade da West Brom a ranar 1 ga watan Yuli da zarar kwanturaginsa ta kare.

An ambato daraktan gudanarwar Kwallon kafa Richard Garlick yana cewa 'mun jima muna bin Craig kuma muna farincikin samun sa'

Daraktan ya kara da cewa tun watan Janairu suka yi kokarin kawo shi West Brom.