Yaya Toure na fushi da Man City

Image caption 'Toure zai iya barin Man City saboda rashin girmama shi da ya ce sun yi'

Mai wakiltar Yaya Toure ya soki hanyar da kulab din Manchester City ya bi wajen taya dan wasan murna a ranar haihuwar sa, da cewa ba ta gamsar ba.

City ta baiwa Toure kek a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Abu Dhabi, sannan kulab din ya taya shi murna a shafin twitter bayan ya cika shekaru 31.

Sai dai Dimitri Seluk ya ce 'Toure ya ji haushi sosai ganin cewa masu kulab din basu taya shi murna kai tsaye ba, ta hanyar gaisawa da shi hannu da hannu a ranar haihuwar tasa.

Kuma ya ce dan wasan zai iya barin su saboda wannan rashin girmamawa da aka nuna masa.

City dai bata ce komai ba a hukumance.