An ci zarafin Balotelli a Italiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sai da 'yansandan da ke wurin suka shiga tsakani domin aikin ba da horon ya ci gaba.

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta kasar Italiya Giancarlo Abete ya yi tir da kalaman nuna wariyar launin fata da aka furta wa Mario Baletoli a wajen ba 'yan wasan kasar horo ranar Laraba.

Wani gungun mutane ne ya furta wa dan wasan gaban na AC Millan kalaman na nuna wariyar launin fata a wajen sansanin ba da horo na Coverciano da ke birnin Florence.

''Wannan hallaya ce da sam ba ta dace ba,'' inji Abete, kuma ya kara da cewa '' wannan bai kamata a ce ya faru ba''.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Balotelli wanda ya je AC Millan daga Manchester City yake fuskantar cin zarafi saboda launi fatarsa ba tun bayan da ya je kasar ta Italiya.

Karin bayani