Brazil 2014: Tawagar Ivory Coast ta isa Amurka

Hakkin mallakar hoto Associated Press
Image caption Sune dai tawagar Afrika ta farko da ta isa Amurka

Tawagar 'yan wasan kwallon kafa na kasar Ivory Coast da za ta je gasar cin kofin Duniya ta isa Birnin Dallas ranar Laraba domin karbar horo.

Kasashen Ghana da Najeriya ma na shirin tafiya kasar ta Amurka domin karbar horon da kuma buga wasanni share fage kafin su karasa zuwa kasar ta Brazil; inda za a soma gasar cin kofin duniya ranar 12 ga watan Yuni.

Kungiyar ta kasar Ivory Coast dai za ta buga wasan sada zumunci da Bosnia a birnin St.louis ranar 30 ga watan Mayu; sannan kuma ta kara da El-Salvador ranar 4 ga Yuni a filin wasa na Frisco da ke kusa ga birnin Dallas.

Hukumar Kwallon Kafa ta kasar Ivory Coast ta ce tawagar za ta rika karbar horo sau 2 a rana a filin na Frisco wanda nan ne gidan kulob din FC Dallas.

Karin bayani