Toure ya nuna alamun barin Man City

Hakkin mallakar hoto
Image caption Toure dai bai ji dadin yadda shugabanin kulob din suka taya shi murnar ranar haihuwarsa ta shafin twitter ba

Yaya Toure ya nuna alamun barin Manchester City da cewar da yayi bai san kowane kulob ne zai buga wa wasa a zangon wasanni na mai zuwa ba.

Wakilin dan wasan na tsakiya Dimitri Seluk ya ce zai iya barin Kulob din saboda yana jin shugabanninsa ba su mutunta shi ba yadda ya kamata.

''Ba mu san gobe ba, amma yanzu na mai da hankali ne ga Gasar cin Kofin Duniya; bayan gasar za mu ga abin da zai faru'' . Inji Yaya Toure mai shekaru 31.

Sai dai ga alamu Manchester City ba ta niyyar barinsa ya tafi ko ma sauraron tayin sayensa daga wasu kungiyoyin saboda har yanzu yana sauran shekaru 3 a kwantaringinsa wadda ya sa wa hannu a watan Aprilun 2013.

Karin bayani