Gomes zai bar Tottenham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A lokacin da Gomes ya isa Tottenham tauraruwarsa ta haska sosai.

Tottenham Hotspur ta sanar da cewa mai tsaron gidanta Heurelho Gomez zai bar kungiyar a karshen kwantaraginsa a watan gobe.

Gomez dan kasar Brazil mai shekaru 33, ya iso kulob din na arewacin London ne a 2008, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen bai wa kungiyar damar kai matakin Kwatafayinal na gasar Zakarun Turai shekaru uku bayan zuwansa.

Sai dai rabon Gomes da buga wa Hotspur wasa tun a watan Nuwamba na 2011 lokacin da ya buga wasa na 135 a kulob din.

''Heurelho Gomez zai bar wannan kungiyar bayan kammala kwantaraginsa a watan gobe kuma muna yi wa wannan mai tsaron gida mai farin jin fatan alheri,'' inji wata sanarwa da Tottenham Hotspur ta fitar a shafinta na intanet.

Karin bayani