Ana bincikar David Moyes

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kafin ya karbi jagoranci kulob din dai, Moyes ya kwashe shekaru 10 yana jagorantar kungiyar Evarton.

'yansanda na bincikar tsohon manajar Manchester United David Moyes sakamakon wani fada da aka yi a wata mashaya da ke Lancashire.

An kira 'yansandan ne zuwa mashayar ta Emporium Bar da ke garin Clitheroe da karfe goma na daren Laraba saboda labarin kai ma wani mutum mai shekaru 23 hari.

'yansandan na yankin Lancashire sun ce ba a yi wa mutumin raunin da zai bukaci yi masa magani a asibiti ba.

A cikin wannan watan na Mayu ne aka sauke Moyes daga mukamin manajan United bayan watanni 10 rike da mukamin.

Karin bayani