'United na bukatar karin 'yan wasa'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Scholes ya aiki karkashin Ryan Giggs a karshen kakar wasan da ta wuce

Manchester United na bukatar karin sabbin 'yan wasa 'biyar ko shida' domin yin takarar lashe gasar Premier ta Ingila.

Tsohon shahararren dan kwallon United, Paul Scholes ne ya bayyana haka.

Scholes yace "Zan kawo dan wasan Bayern Munich Toni Kroos amma kuma United na bukatar karin manyan 'yan wasa biyar ko shida".

Dan shekaru 39, Schole ya yi aiki karkashin Ryan Giggs a wasanni da ya jagoranci United, amma kuma ya ce ba ya tunanin akwai rawar da zai taka a kungiyar a kakar wasa mai zuwa.

Karin bayani