'Zan iya zama a Man City har mutuwa'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Toure dai bai ji dadin yadda shugabanin kulob din suka taya shi murnar ranar haihuwarsa ta shafin twitter ba.

Dan wasan tsakiya na Manchester City, Yaya Toure, ya ce zai iya zama a kulob din har karshen rayuwarsa; idan aka ba shi tabbacin ci gaba da aiki da shi har illa masha'allahu.

Dan wasan mai shekaru 31 ya ce ya fusata kwarai da abin da ya ke jin rashin mutuntawa ne daga shugabannin kungiyar, kuma ya nuna alamun zai bar ta ranar.

Amma yanzu wakilinsa Dimitri Seluk ya ce Toure na son zama a kulob din har illa masha'allahu in har za a yi masa yadda Real Madrid ta yi wa Zinedine Zidane.

Zidane dai ya zamo mai ba da shawara kuma kocin Real Madrid bayan ya yi ritaya daga buga wasa.

Karin bayani