PSG na tattaunawa da David Luiz

Image caption David Luiz

Chelsea na tattaunawa da zakarun kwallon Faransa, Paris St-Germain don cinikin dan wasan baya David Luiz a kan kusan fan miliyan 40.

Dan shekaru 27, Luiz ya koma Chelsea ne daga Benfica a kan fan miliyan 21.3 a watan Janairun 2011.

Dan wasan Brazil din ya taka leda a wasanni 143 a Stamford Bridge.

Luiz na da sauran shekaru uku a yarjejeniyar shekaru biyar da ya kulla a Chelsea.

Barcelona na daga cikin kungiyoyin da ke nuna sha'awar sayen Luiz.

Karin bayani