Ghana ta sabuntawa Appiah kwangilarsa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kwesi Appiah zai iya kafa tarihi a Brazil

Hukumar kwallon Ghana ta tsawaitawa kocin tawagar Black Stars, Kwesi Appiah kwangilarsa har zuwa watan Yulin 2016.

Shugaban hukumar kwallon Ghana, Kwesi Nyantekyi ya shaidawa BBC cewar sun dauki matakin ne saboda ganin kwazon kocin mai shekaru 53.

Ya ce "Wannan sabuwar kwangilar ta nuna cewar muna da kwarin gwiwa a kan Appiah a gasar cin kofin duniya".

Appiah wanda tsohon kyaftin din Black Stars ne, an bashi mukamin ne a watan Afrilun 2012.

Zai kasance dan kasar Ghana na farko da zai jagoranci Black Stars zuwa gasar cin kofin duniya.

Karin bayani