Shola Ameobi ya bar Newcastle

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shola Ameobi

Kungiyar Newscastle ta Ingila ta sallami Shola Ameobi bayan shafe shekaru 14 tare da kungiyar.

Dan shekaru 32, ya bugawa Newcastle wasanni 397 inda ya zura kwallaye 79.

Ameobi na daga 'yan kwallon da Nigeria ta gayyata don buga gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil.

Yana cikin 'yan kwallo tara da Newcastle ta sallama bayan kawon karshen yarjejeniyarsu da kungiyar.

Ameobi ya soma bugawa Newcastle leda ne a watan Satumbar shekara ta 2000 kuma ya zura kwallo a ragar Barcelona a wasan zakarun Turai a watan Disambar 2002.