Kofin Duniya: Spain ta kirawo Deulofeu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kiran nasa zai bashi damar maye gurbin wani dan wasan

Spain ta gayyaci dan wasan tsakiya na Barcelona wanda ya yi kakar wasa ta 2013-14 a zaman aro a Everton domin buga wasan sada zumunta na kafin gasar Kofin Duniya.

Dan wasan mai shekara 20 wanda bai taba buga wa babbar kungiyar kasar Spain wasa ba, yana cikin 'yan wasa 19 da za su kara da Bolivia a Seville ranar 30 ga watan Mayu.

Deulofeu ya yi rawar gani a Everton, inda ya ci kwallaye uku a wasannin Premier 25 da aka sa shi.

Ranar 2 ga watan Yuni kocin Spain Vicente del Bosque zai bayyana 'yan wasan kasar 23 da za su gasar cin Kofin Duniya a Brazil.

Tuni kociyan ya sanar da tawagar 'yan wasan 30 kuma a karshen wannan makon ne ake saran zai rage bakwai.

Babu wani dan wasan Real Madrid ko na Atletico Madrid a cikin 'yan wasan na Spain da za su kara da Bolivia