Gerrad: zan yanke shawara bayan kofin Duniya

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Gerrard ya ce, ''ba zan ci gaba da zama ba idan ba a bukata ta''

Steven Gerrard ya ce zai yanke shawara ko zai ci gaba da yi wa Ingila wasa ko kuma zai daina bayan gasar Kofin Duniya ta Brazil.

Kyaftin din na Ingila mai shekaru 33 zai tattauna da kocin kasar Roy Hodgson da kuma na kungiyarsa Liverpool Brendan Rodgers bayan gasar kafin ya yanke shawara.

Ya ce, komai zai dogara ne ga yadda gasar za ta kasance, kokarin da na yi, wasan da kungiyar ta yi, za a ci gaba da bukata ta bayan gasar ta Duniya?

Ingila za ta yi wasan sada zumunta da Peru a Wembley ranar 30 ga watan Mayu kafin ta tafi Miami ta kara wasan shiri da Ecuador da Honduras.

Kocin kasar Roy Hodgson na ganin tawagar Ingila ta bana ta fi wadda ya kai gasar cin Kofin Turai ta 2012.