Kofin Duniya: Tetoun ta samu shiga

Image caption A watan Disamba Morocco za ta karbi bakuncin gasar ta Kofin Duniya na Kungiyoyi

Moghreb Tetoun ta samu nasarar daukar kofin gasar league din Morocco da hakan ya ba ta damar shiga gasar cin Kofin Duniya na kwallon kafa na kungiyoyi a matsayin zakarun mai karbar bakunci.

Kungiyar ta samu nasarar ce a wasansu na karshe na kakar nan da Renaissance Berkane, yayin da Raja Casablanca da ke bin ta a baya ta sha kashi a hannun Olympique Safi.

Tetoun din ta kammala kakar ta bana da bambancin maki uku tsakaninta da masu rike da kofin League din na Morocco Raja.

Raja ce ta biyu a gasar cin Kofin Duniyar ta 2013 da ta yi rashin nasara 2-0 a wasan karshe da Zakarun Turai Bayern Munich na Jamus.

Sabbin zakarun Turai Real Madrid da zakarun Amurka ta Arewa da ta tsakiya Cruz Azul ta Mexico da kuma Auckland City ta New Zealand zakarun Oceania dukkanninsu sun samu nasarar samun gurbi a gasar ta bana.