Lallana-"ba ruwana da jita-jita"

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption ''Yanzu hankalina ya koma ne kan rawar da zan taka wa Ingila a gasar kofin duniya''

Dan wasan Southampton Adam Lallana ya ce jita-jitar da ake yadawa dangane da cigaba da zamansa a kungiyar ba za ta dauke masa hankali daga wasan da zai yi wa Ingila ba.

Dan wasan mai shekaru 26 na cigaba da shirye shiryen tunkarar gasar kofin duniya wadda za a fara a ranar 12 ga watan Yuni, yayin da Liverpool ke nuna alamun sayen shi.

Lallana ya ce, "ba bu wani bambanci kan makomata kafin ko bayan kammala gasar cin kofin duniya."

Dan wasan wanda ya shiga kulob din Southampton a shekarar 2000, ya kuma ci kwallaye 10 a wasanni 42 da ya buga a gasar kakar da ta kare inda ya taimaka wa kulob din ya kai mataki na 8 a gasar premier.