Pique ya tsawaita kwangilarsa a Barca

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gerard Pique

Dan kwallon Barcelona Gerard Pique ya sanya hannu a yarjejeniyar tsawaita buga kwallo a Nou Camp zuwa karin shekaru hudu.

Dan wasan mai shekaru 27 kenan zai ci gaba da taka leda a Barca har zuwa shekara ta 2019

Pique ya ce "Barcelona na da abubuwan da take bukata don samun nasarori".

Pique ya buga kwallo a Manchester United daga shekara ta 2004 zuwa 2008.

Ya buga wasanni 266 tare da Barca sannan kuma ya lashe kofunan La Liga hudu da na zakarun Turai biyu.

Karin bayani