'Ingila ta koyi salon wasan Liverpool'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gerrard da Sterling da kuma Henderson

Tsohon dan kwallon Manchester United Paul Scholes ya bukaci kocin Ingila ya koyi salon wasan Liverpool a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Scholes yace "Ina son Ingila ta murza leda kamar Liverpool, ta dunga kai hare-hare cin kwallo".

A cewarsa kungiyar Liverpool ta haskaka a kakar wasa ta bana.

Liverpool ta kara nuna karfinta a kwallon kafa a karkashin jagorancin Brendan Rodgers inda ta karke ta biyu a kan teburin gasar.

'Yan wasan Liverpool da ke cikin tawagar Ingila su ne; Steven Gerrard, Daniel Sturridge, Raheem Sterling, Jordan Henderson da kuma Glen Johnson.

Karin bayani