Fifa ta damu kan filaye uku a Brazil

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daya daga cikin filayen da za a murza leda a Brazil

Babban sakataren hukumar kwallon kafa ta duniya Jerome Valcke ya nuna damuwarsa kan batun kamalla gina wasu filayen wasa uku da za a yi wasanni gasar cin kofin duniya cikin su a Brazil.

A ranar 12 ga watan Yuni ake soma gasar.

Valcke ya bayyana fargabarsa ta sa ne a Natal da Porto Alegre da Sao Paulo ina da za a bude gasar a yayinda za a fafata tsakanin Brazil da Croatia.

Ya kuma bayyana cewa Natal's Arena das Dunes suna neman yin "gudun wuce sa'a."

Valcke ya kara da cewa "Muna bukatar karin azama da mai da hankali daga kowane bangare na Natal don tabbatar da ganin komai ya kammalu an kuma yi gwaji."

Haka nan Vackle ya ce masu shirya abubuwa a Arena Fonte Nova da ke Salvador ba su da isasshen lokaci kafin fara wasannin rukunin su na farko a sake wasan karshe na shekarar 2010 tsakanin kasar Spain da Netherland a ranar 13 ga watan Yuni.

Ya kuma yi jan hankali inda yace "ya zama wajibi komai yan zama an kammala shi a wannan ranar."

Karin bayani