Za a koma tattaunawa kan Luke Shaw

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Luke Shaw ya haskaka a kakar wasa ta bana

Kulob din Manchester United da na Southampton za su ci gaba da tattaunawa kan batun sayen dan wasan baya na gefen hagu Luke Shaw a ranar Juma'a.

Tuni dai Saints ta ki amsar tayin fam miliyan 27 kan dan wasan mai shekaru 18.

United na matukar son sayen dan wasan baya mai buga gefen hagu.

A halin yanzu Patrice Evra wanda ke rike da gurbin ya rattaba hannu kan sabuwar kwantaragi don ci gaba da taka leda a Old Trafford.

Baya ga Shaw wani dan wasan Southampton da ake ganin zai bar kulob din shi ne Adam Lallana wanda Liverpool da Tottenham ke zawarcinsa.

A yayinda shi kuma Paul Lambert zai bar Southampton din zuwa Liverpool.

Karin bayani