Wenger zai kasance a Arsenal har 2017

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan wasan Arsenal na jinjinawa Arsene Wenger

Arsene Wenger ya amince da sabunta kwantaragin shekaru uku a matsayin kocin Arsenal wacca za ta kare a shekarar 2017.

Za dai a rattaba hannu kan kwantaragin a ranar Asabar.

Wenger, mai shekaru 64 ya jagoranci Arsenal ta lashe manyan kofuna 8 daga lokacin da ya fara jagoranyar kulob din a shekarar 1996.

A wannan kakar da ta kare ya jagoranci Arsenal ta lashe gasar cin kofin FA.

Sannan kulub din ya tsallake zuwa gasar zakarun Turai har sau 18 a karkashin jagorancinsa.

Kafin nasarar da ta samu kwana nan na cin kofin FA, rabon Arsenal da daga wani muhimmmin kofi tun shekarar 2005.

Karin bayani